Za a cigaba da tsare Muhammed Morsi

Image caption Magoya bayan Muhammed Morsi

Hukumomin Masar sun bada umarnin ci gaba da tsare hambararren shugaban kasar Mohammed Morsi kan zargin cin amanar kasa yayin da a waje guda ake ci gaba da gangamin dubban masu adawa dana magoya bayansa.

Ana zargin Mista Morsi da hada baki da mayakan Paladinawa na Hamas wajen kai hare-hare a gidajen yari, inda aka saki wasu masu kishin Islama lokacin boren hambarar da Hosni Mubarak a shekara ta 2011.

Tun lokacin da aka hambarar da Mohamed Morsi a farko wannan watan ba a kara ganinsa a bainar jama'a ba.

Birnin Alkahira na cike da sojoji da tankunan yaki da motoci masu sulke,gabanin abinda ake ganin babban fito na fito ne tsakanin bangarorin biyu.

Karin bayani