Zanga-zangar adawa da gwamnatin Tunisia

Image caption 'Yan adawa da gwamnati

Dubban al'ummar Tunisia ne suka taru a babban birnin kasar Tunis, inda suka rika rera wakokin kin jinin gwamnatin kasar mai ra'ayin Musulunci kwana daya bayan kisan wani jigon 'yan adawar kasar.

Wakilan 'yan adawar na bukatar gwamnatin Ennahda ta sauka daga karagar mulki inda suke zarginta da hannu a kisan jagoran yan adawa Muhammad Brahmi.

Tun da farko yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar.

Zanga-zangar dai ta yi kama da wadda aka yi a kasar watanni shida da suka gabata, a lokacin da aka kashe wani jigon 'yan adawa Chokri Belaid.

Karin bayani