An harbe mai fafutuka a Libiya

Image caption An kashe wani mai fafutuka a Libiya

An harbe har lahira wani fitaccen mai fafutuka a Libiya Abdslam Al Mismari, a gabashin birnin Benghazi.

Wannan shine kisa na farko da aka yiwa wani mai fafutuka a birnin, abinda ya janyo Allah wadai daga bangarori da dama.

Mr Al -Mismari na cikin wadanda suka soma yin bore da ya yi sanadiyyar hambarar da gwamnatin marigayi Mo'ammar Gaddafi, sannan kuma yake sukar kungiyoyin dake dauke da makamai a cikin kasar, wadanda suka ki ajiye makamansu bayan juyin juya halin.

Yana kuma kin jinin kasancewar kungiyar 'yan uwa musulmi a Libyan.

Birnin Benghazi dai, na fuskantar tashe-tashen hankula tun bayan kifar da gwamnatin Kanal Gaddafi da suka hada da harin da aka kai; kan ofishin jakadancin Amurka a watan Satumba da ya yi sanadiyyar kisan jakadan Amurka da wasu Amurkawan su uku.

Karin bayani