Magoya bayan Morsi sun yi zaman-dirshan

Image caption Magoya bayan Morsi

Magoya bayan hambararren shugaban Masar Mohammed Morsi sun cigaba da zaman darshan a harabar masallacin Rabaa al-Adawiyya a gabashin birnin Alkahira.

Wakilin BBC dake harabar masallacin yace yanzu kura ta lafa bayan zubar da jinin da aka yi a jiya Asabar.

Da yake jawabi a bikin yaye dalibai a makarantar horar da yan sanda dake birnin Alkahira, Ministan cikin gida Mohammed Ibrahim yace jami'an tsaro za su sanya kafar wando daya da duk wanda ya nemi tada fitina.

Masu zanga-zangar a kusada masallacin sun ce ba zasu tashi ba har sai an biya musu bukatarsu ta maidoda Muhammed Morsi a kan mulki.

Karin bayani