A Libiya fursunoni sama da 1000 sun arce

Image caption A Libiya fursunoni sama da 1000 sun arce daga gidan-yari

Fursunoni da dama ne suka tsere daga wani gidan yari a birnin Benghazin Kasar Libya.

Anyi kiyasin cewa kimanin fursunoni dubu daya da dari biyu ne suka tsere daga gidan yarin na Alkwafiya a ranar Asabar.

Fursunonin sun hada da wadanda ake tunanin magoya bayan Marigayi Mu'ammar Gaddafi ne.

Ana zarginsu ne da kai hari ga sansanonin jami'an tsaro ,bayan yakin basasar kasar.

Wani mai magana da yawun jami'an tsaro ya shaidawa BBC cewa an kamo wasu daga cikin fursunonin, amma bai fadi yawansu ba.

Karin bayani