Bama-bamai sun tashi a Benghazi

Image caption Benghazi

Wasu bama-bamai sun fashe a gaban wasu kotuna biyu, a tashin hankali na baya-bayan nan da ake yi a birnin Benghazi na Libya.

Wasu mutane goma dake zaune a kusa da kotunan sun samu raunuka, sakamakon fashewar bama-baman wadanda suka lalata wani sashe na daya daga cikin Kotunan.

Wani jami'in tsaro a birnin Benghazin ya ce, yana jin wasu daga cikin fursunoni dubu 200 ne da suka tsere daga gidan Yarin a ranar asabar suka dasa bama-baman.

A dan tsakanin nan dai an kashe mutane da dama da suka hada da wani babban mai fafutuka a cikin birnin.

Ministan Shari'a na kasar ta Libya ya ce kasarsa za ta nemi agajin kasashen waje.