Zaben shugaban kasa a Mali

Image caption 'Yan Mali sun fara kada kuriar zaben shugaban kasa

Ana cigaba da kidaya kuri'u na zaben Shugaban kasa a Mali, zaben da ake fatan zai maida kasar kan turbar democradiyya, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a bara.

Wadanda suka sa ido a zaben sun ce mutane da dama sun fito don kada kuri'unsu a Bamako babban birnin kasar, da sauran wasu sassa na kudanci.

Sai dai kuma rahotanni sun ce a yankin arewaci mutanen da suka fita ba su da yawa.

Wakilin BBC ya ce mutane da dama a can sun ce kada a diga musu tauwada a hannu, shaidar dake nuna cewa sun yi zabe.

Wakilin namu yace Azbinawa wadanda har yanzu ke iko da wasu sassan arewacin kasar, sun nuna adawa da zaben, ko da yake sun amince a kada kuri'ar.

Wakilin BBC yace wasu 'yan Kasar Mali sama da miliyan shida ne, za su yanke shawarar wanda za su zaba cikin 'yan takara 27.

Karin bayani