An fitar da kudin kujerun aikin hajji

Hukumar da ke kula da aikin Hajji ta Najeriya ta sanar da kudin kujerun aikin hajjin bana.

Ta ce an samu kari a kudin kujerun aikin hajjin fiye da bara, ko da yake ta ce karin ba mai yawa ba ne.

Hukumar ta ce kudin karamar kujera ta zartar naira dubu dari shida, yayin da babbar kujera ta zarta naira dubu dari bakwai.

Hukumar ta ce karin ya biyo bayan karin da aka samu wajen canza naira zuwa dala, a kasuwar musayar kudaden waje, da kudin masauki a garin Makka.

A kowacce shekara dai maniyyata aikin hajji su kan gamu da matsaloli, lamarin da ya sanya ko a bara sai da hukumomin Saudiyya suka mayar da dubban Mata maniyyata 'yan Najeriya gida, saboda rashin muharramai.