Mutane akalla 30 ne aka kashe a harin Kano

Kano Nigeria
Image caption Gwamnan Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso

Mutane akalla talatin ne suka hallaka sakamakon fashewar wasu abubuwa a birnin na biyu mafi girma a arewacin Nigeria

Rahotanni sun ce an samu tashin bama-bamai ne da misalin karfe tara na daren jiya a wurin matattaran mutanen da suke zaune a unguwar Sabon Gari dake Kano.

Shaidu sun ce abubuwa masu fashewa gudu uku zuwa hudu ne suka fashe a unguwar ta Sabon Gari kuma an ji kararsu a wurare da dama.

Wakilin BBC ya ce wannan shi ne hari mafi girma tun bayan wanda aka yi ranar ashirin ga watan janairu na bara wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dari