Fursunoni fiye da 200 sun tsere a Pakistan

Taliban
Image caption Mayakan kungiyar Taliban

Wani jami'in gwamnati a Pakistan ya ce fursunoni fiye da dari biyu da suka hada da mayaka 'yan kishin Islama 30 sun tsere bayan wasu hare-hare da 'yan Taliban masu tayar da kayar baya suka kai lokaci daya a kan wani gidan Yari dake arewa maso yammacin kasar.

Jami'in Mushtaq Jadoon ya shaidawa wani gidan talabijin cewar 'yan taliban din kimanin 60 ne suka kuutsa kai da karfi a gidan Yarin, yayinda wasu saura suka rinka harba manyan harsasai da makaman roka a gaban gidan yarin.

Mr Jadoon yace an kashe a kalla mutane 12 da suka hada da yan sanda 4 a harin.