Addu'o'in jana'iza a Spain

Tunawa da mamata
Image caption Tunawa da mamata

Daruruwan mutane sun gudanar da addu'o'i a babban cocin birnin Santiago de Compestela na arewa-maso-yammacin kasar Spain, domin tunawa da wadanda hadarin jirgin kasa ya rutsa dasu a makon jiya.

Mutane 79 ne su ka hallaka.

'Yan gidan sarautar Spain din da kuma manyan jami'an gwamnati sun halarci taron gudanar da addu'o'in.

Bayan addu'o'in, Yarima da kuma Praministan kasar, Mariano Rajoy, sun yiwa iyalan wadanda suka rasun jaje.

Ana sa ran cewa 'yan uwan wadanda hadarin ya rutsa da su za su samu kusan dala dubu 80 a matsayin diyya akan kowane mutum daya.

A ranar Lahadi, wani alkali yace matukin jirgin, Francisco Jose Garzon, zai iya fuskantar tuhumar kisan kai ta hanyar ganganci.

Karin bayani