IBK ne ke kan gaba a zaben Mali

IKB a lokacin da ya kada kuri'arsa
Image caption IBK zai iya lashe zaben a zagayen farko

Ma'aikatar cikin gida ta kasar ta ce bayan an kidaya kashi 1 cikin 3 na kuru'un da aka kada, sakamakon farko ya nuna cewa dan takarar jam'iyyar RPM, Ibrahim Boubacar Keita, wanda ake yiwa lakani da IBK, shi ne ke kan gaba da tazara mai yawa a zaben shugaban kasar da aka yi.

A wani taron manema labarai, Ministan cikin gida na kasar ta Mali, Kanal Moussa Sinko Coulibaly ya ce idan sakamakon ya cigaba da kasancewa haka, to Ibrahim Boubacar Keita ne zai lashe zaben tun a zagayen farko.

A halin da ake ciki kuma, shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara wanda har illa yau shi ne shugaban kungiyar ECOWAS, ya nuna kwarin gwiwa cewa duka 'yan takarar 27 za su amince da sakamakon da Hukuma za ta bayar.

Gobe Laraba ne dai ake sa ran za a bayyana kammalallen sakamakon zaben.

Karin bayani