Kotun soja a Amurka ta sami Manning da laifi

Bradley Manning
Image caption Bradley Manning

Wata kotun soji a Amurka ta samu sojan kasar Bradley Manning da aikata laifuka 20 masu alaka da leken asirin kasa.

To amma ba ta same shi da laifi a babbar tuhumar da ake masa ba ta taimakon abokan gaba.

An zarge shi ne da mika dubun dubatar takardun sirri ga shafin nan na yanar gizo mai tsegunta bayanan sirri na Wikileaks.

A gobe Laraba ne alkalin zai yi shelar hukuncin da kotun ta zartar a kansa . Manning dai na fuskantar daurin gida yari har na tsawon shekaru 136.

Shafin na Wikileaks ya ambaci samunsa da laifi da aka yi a matsayin "tsattsauran ra'ayin tsaron kasa mai hadari".

Karin bayani