INEC ta yi wa jam'iyyar APC rajista

Image caption Jam'iyyar adawa ta APC

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya wato INEC ta yiwa jam'iyyar adawa ta APC rajista a matsayin jam'iyyar siyasa.

Sanarwar da Sakataren INEC, Abdullahi Kaugama ya sanyawa hannu, ta ce daga yanzu jam'iyyar APC na daga cikin jam'iyyun siyasar Najeriya.

Wannan mataki dai na nufin daga yanzu jam'iyyun adawa na ACN da ANPP da CPC sun dunkule wuri guda.

A cewar hukumar ta INEC, a yanzu za ta janye rajistar data yiwa wadannan jam'iyyun da suka dungule.

Jam'iyyun adawar dai sun yanke shawarar hadewa wuri guda ne domin tunkarar jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya a zaben shekara ta 2015.

Karin bayani