Kokarin kare hakkin fasinjojin jiragen sama

Image caption Sufurin jiragen sama a Najeriya

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman Najeriya NCAA tace, ta bullo da tsarin kare hakkokin fasinjojin jiragen sama a kasar.

An dai jima fasinjoji a Naijeriya suna zargin cewa, akasarin kamfanonin jiragen sama ba sa mutunta hakkokin fasinjojinsu kama mayarwa fasinjoji kudadensu na tikiti bayan rasa jirgi, ko kamfanin jiragen sama ya samarwa fasinja masauki in jirgin yayi jinkiri ko an soke tashinsa.

A cewarta hukumar NCAA, duk kamfanin da ya jinkirta daukar fasinja, to dole ne ya dauki dawainiyar fasinjan har sai an samu wani jirgin da zai dauke shi.