An kara wa'adin kwamitin sulhu da Boko Haram

Bioko haram
Image caption Abubakar Shekau shugaban kungiyar da ake kira boko haram

Shugaba Goodluck Jonathan ya kara wa kwamitin da ke kokarin sulhu da 'yan kungiyar Jama'atu Ahlis Sunnah lid Da'awati wal Jihad, wacce ake kira Boko Haram, karin wa'adi na tsawon watanni biyu.

Sai dai lamarin na zuwa ne a dai dai lokacin da wasu 'yan kasar ke sukar kwamitin a kan cewa ya gaza wajen sauke wajibcin da aka dora masa, saboda sun yi zargin cewa kwamitin ya yi ikirarin cimma yarjejeniyar dakatar da hare-hare da 'yan kungiyar, amma daga bisani shugaban Kungiyar, mallam Abubakar Shekau ya musanta.

Sai dai kwamitin a na sa bangaren ya bayyana cewa ya cimma nasarori da dama ta bangaren tattaunawa da 'yan kungiyar da kuma batun tsugunar da wadanda suka amince da shirin ahuwa.

Shugaban kwamitin, wanda shi ne Ministan ayyuka na musamman Alhaji Kabiru Tanimu Turaki ya ce mutane basu fahimci cewa aikin da suke yi abu ne da ya shafi tsaro ba saboda mutane da suke tattaunawa da su ba za su so a fadi wasu abubuwa ba.