Makon shayar da jarirai nonon uwa zalla

Image caption Jarirai na bukatar nono zalla

Daga ranar daya zuwa bakwai ga watan Agusta a duk shekara ake bukin shayar da jarirai nonon uwa zalla a duniya.

Ana bukinne a kasashe fiye da 170 a fadin duniya don inganta lafiyar kananan yara ta wannan hanyar.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bada shawarar a shayar da jarirai nonon uwa zalla har zuwa watanni shida na farko daga haihuwa, sannan a cigaba da bada nonon hade da abinci har zuwa jarirai sukai shekaru biyu a duniya.

A cewar masana harkokin kiwon lafiya, wannan matakin zai kara lafiya ga jarirai da kuma ita kanta uwa.

Hukumar WHO din kuma ta bukaci gwamnatocin kasashe su bada gudun muwa don cimma burin da aka sa a gaba.