2015: Sama ta yi wa Yaro nisa —PDP

Image caption Manyan jam'iyyun siyasar Najeriya

Jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya ta maida martani dangane da rajistar da hukumar zaben Najeriya-INEC ta yi wa jam'iyyar adawa ta APC.

A cewar PDP suna murna da matakin, kuma basa zullumin rasa mulki saboda sun shafe shekaru 15 suna mulkin kasar kuma 'yan adawa ba zasu iya kwace mulkin ba.

Sanata Abubakar Gada wanda ke baiwa shugaban jam'iyyar PDP na kasa shawara, ya ce "harkar demokradiya kamar masabaka ce, kowa zai baje kolinsa ga 'yan Najeriya don su zaba".

PDP ta kara da cewar "sama ta yi wa Yaro nisa".

Anasu bangaren, daya daga cikin jam'iyyun adawar da suka dunkule wajen kafa sabuwar jam'iyyar APC, wato ACN ta ce rajistar ta share musu hanyar kalubalantar jam'iyyar PDP mai mulki , tare da kwace mulki daga hannunta.

Sanata Lawal Shuaibu na tsohuwar jam'iyyar ACN din ya ce "an buda mana hanya don kalubalantar PDP don mu ceci kasar nan daga tabarbarewa".

A cewar 'yan adawan za su hada kai don ganin sun cimma burinsu.

Karin bayani