'Yan Majalisar Uruguay sun halarta tabar wiwi

Image caption Ganyen tabar wiwi a kasar Uruguay

Majalisar Wakilan kasar Uruguay ta kada kuri'ar amincewa da halatta Marijuana ko kuma tabar wiwi.

Idan har Majalisar dattawa ta goyi bayan wannan matakin, kasar ta Uruguay za ta zamo kasa ta farko a duniya da ta hallata noma da sayarwa da kuma amfani da tabar ta wiwi.

Majalisar wakilan dai sai da ta shafe sama da sa'oi goma sha uku tana tafka muhawara kan shirin dokar.

Za a kyale 'yan kasar ta Uruguay wadanda shekarun su suka zarce goma sha takwas su rinka sayen tabar ta wiwi kilo 40 a kowani wata.

Wannan kudurin idan ya zama doka bai shafi baki 'yan kasar waje dake Uruguay ba.

Shugaba Jose Mujica ya ce halatta shan tabar ta wiwi zai rage karfin dillalanta, to amma masu adawa da shirin sun zargi gwamnatin da yin wasa da wuta.

Karin bayani