Berlusconi ya soki hukuncin Kotu

Tsohon Fira Ministan Italiya Silvio Berlusconi
Image caption Tsohon Fira Ministan Italiya Silvio Berlusconi

Tsohon Fira Ministan Italiya Silvio Berlusconi, ya fitar da wani sakon faifan bidiyo na bacin rai, kan hukuncin da Kotun Kolin kasar ta yanke masa.

Kotun kolin ta yanke masa hukuncin dauri kan aikata laifin kaucewa biyan haraji.

Mr Berlusconi ya ce, ya kasance wanda aka sha yiwa jerin zarge-zarge da fuskantar shari'a masu daure kai da basu da kanshin gaskiya.

Me yiwuwa ne a yiwa Mr Berlusconi daurin talala a gidansa, ko kuma a sa shi yin wasu aikace-aikacen horo, na yi wa al'umma hidima, maimakon zaman jarun a bisa la'akari da shekarunsa.

Mr Berlusconi dai ya zargi sashen shari'a na kasar Italiyar da wuce gona da iri.

Ya ce hukunci ya tabbatar masa da irin yadda ake cewa wani bangare da sashen shari'ar kasar ya zama kara zube, mai cike da alkalan da suke 'yan amshin shata.

Alkalan dai sun bukaci kotun ta yi la'akari da hukuncin baya, na cewa ya kamata a duba yiwuwar haramta masa rike duk wani mukami na gwamnati.

Sai dai bayanai na nuni da cewa har yanzu Mr Berleconi na da karfin fada a ji a kasar, kana akwai fargabar cewa haramta masa shiga harkokin siyasa ka iya kawo rashin tabbas a gwamnatin Italiyar.