'Yan Boko Haram na shirin kai hari- JTF

Image caption Imam Shekau

Rundunar tsaro ta hadin gwiwa-JTF a jihar Borno ta bukaci mazauna jihar su farga, saboda shirin 'yan kungiyar Boko Haram na kaddamar da hare-hare daga yanzu har zuwa lokacin bukukuwan karamar Sallah.

Kakakin JTF a jihar, Laftanar Kanar Sagir Musa a wata sanarwa, ya ce 'yan Boko Haram na shirin kaddamar da hare-hare a Maiduguri da kewaye daga yanzu zuwa ranar Sallah.

Sanarwar ta bukaci jama'a su kasance cikin shiri kuma su lura da yanayin da suke a irin wannan lokacin.

A cewar sanarwar duk da dai an rage dokar hana fitar dare daga karfe 11 na dare zuwa 6 na safe, jami'an tsaro na ci gaba da kokarin tabbatar da tsaron lafiyar jama'a da dukiyoyinsu.

Jihar Borno ta kasance matattarar 'yan Boko Haram abin da yasa ake zaman dar dar a tsakanin al'umma.

Karin bayani