An kashe akalla mutane 8 a Jalalabad

'Yan sanda a inda aka kai harin
Image caption Harin ya shafi Jami'in tsaron Afghanistan da fararen hula

Akalla mutane takwas aka kashe a wani harin kunar bakin wake da aka kai kusa da ofishin jakadancin India dake gabashin birnin Jalalabad a Afghanistan.

Jami'ai sun ce masu gadin ofishin sun harbi biyu daga cikin maharan.

Wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen India Syed Akbaruddin ya ce wadanda harin ya shafa, sun hada da jami'in tsaron Afghanistan da kuma wasu fararen hula.

Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan da Amurka ta bada umarnin rufe ofisoshin jakadancinta musaman a yankin gabas ta tsakiya da kuma Arewacin Afirka, bayan da ta yi imanin cewa kungiyar Al- Qaida na shirye shiryen kaiwa ofisoshinta jerin hare hare a ranar lahadi.

Ofishin jakadancin Amurka dake Kabul zai kasance a rufe ranar lahadi, a wani bangare na daukar matakin tsaro.

Karin bayani