Wasu Kasashen Turai zasu rufe ofisoshinsu a Yemen

Yemen
Image caption Kasashen Turai na fargabar kaiwa ofisoshinsu hari

Kasashen Turai da dama sun sanar da rufe ofisoshin jakadancinsu na wucin gadi a Yemen saboda dalilai na tsaro.

Kasashen Faransa da Jamus da Burtaniya sun ce zasu rufe dukkanin ofisoshinsu a Sanaa a ranakun hudu da biyar na watan Agusta.

Ba a bayyana cikakken bayanin zargin barazanar da akai musu ba.

A ranar juma'a Amurka ta bada umarnin rufe ofisoshin jakadancin ta musaman a daukacin yankin gabas ta tsakiya da kuma Arewacin Afirka, bayan da sukai imanin cewa kungiyar Al- Qaida na shirin kai jerin hare hare.

Karin bayani