Khameni ya nuna goyan baya ga Rouhani

Hassan Rouhani
Image caption Ranar Lahadi Rouhani zai yi rantsuwa a majalisar dokoki

Jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya bada cikakken goyon bayansa ga sabon Shugaban Kasar, Hassan Rouhani, a lokacin bikin da aka gudanar yau a Tehran.

Ranar lahadi idan Allah ya kaimu ne Hassan Rouhanin zai yi rantsuwar kama aiki a majalisar dokokin Kasar.

A watan Yunin da ya wuce ne mista Rouhani ya bada mamaki, yayin da ya lashe zaben Shugaban Kasar tun zagaye na farko.

A lokacin yakin neman zabensa ya yi alkawarin zai yi sauye-sauye idan yayi nasara, kuma zai kawo karshen halin saniyar waren da kasashen duniya suke wa Iran.

Sai dai a cewar wakilin BBC a Iran, jagoran addinin Iran ne, Ayatollah Ali Khamenei mai yanke magana, ba wai shugaba Hassan Rouhani ba.

Karin bayani