China ta daina sayen madara daga New Zealand

Madarar gari
Image caption Ana fargabar samun karancin madara a China

New Zealand ta ce, China ta dakatar da shigo da madarar gari daga kasar ta New Zealand, bayan an fada mata cewa, akwai yiwuwar wata madarar na dauke da wata kwayar cuta da ka iya hallakarwa.

Kasashe irinsu Rasha da Thailand su ma sun dauki irin wannan mataki, bayan da kamfani mafi girma wajen samar da madara a New Zealand, wato Fonterra, ya sanar da abokan cinikayyarsa a fadin duniya irin hadarin da ke tattare da shan madarar.

China tana sayo kusan kashi tamanin bisa dari na madarar gari daga New Zealand.

Hakan ya sa ake fargabar samun karancin madarar a Chinar.

Karin bayani