Magoya bayan Morsi zasu ci gaba da zanga-zanga

Tattaunawa da shugananin rikon kwaryar kasar Masar
Image caption Tattaunawa da shugananin rikon kwaryar kasar Masar

Magoya bayan shugaba Morsi na Masar sun ce za su ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tunbuke shin da sojojin kasar suka yi.

Sun ce za su kuma nemi a sake mayar da shi bisa karagar mulki.

Wannan ya biyo bayan tattaunawa da mukaddashin sakataren harkokin wajen Amurka, William Burns, inda ya gana da shugabannin gwamnatin rikon kwaryar kasar.

Mr William Burns, da manzo na musamman na Tarayyar Turai Bernardino Leo, sun gana da shugaban rikon kwarya na kasar ta masar Adly Mansour, da mataimakinsa Mohammed El Baradei da kuma Ministan harkokin wajen kasar ta Masar Nabil Fahmi.

Mr Fahmi ya ce gwamnati ba zata nuna karfin tuwo kan masu zanga-zangar ba, har sai idan abin ya kai makura.