Uganda ta nemi a tura karin Sojoji Somalia

Sojojin Tarayyar Afirka
Image caption Uganda na son ganin an jibge karin sojoji fiye da dubu biyu

Uganda ta yi kiran da a kara tura wasu dakarun Tarayyar Afirka zuwa Somalia, domin su kare yankunan da aka kwace daga mayakan Islama na Al- Shabaab, wadanda a da su ke rike da galibin yankunan kasar.

Ministan harkokin Ugandar ya ce, ya kamata a karo sojoji fiye da dubu biyu, ta yadda yawan dakarun Tarayyar Afirkar a Somalia zai kai dubu ashirin.

Shugabannin Kasashen da suka yi karo-karon sojojin suna ganawa da Shugaban Somalia a Kampala, babban birnin Uganda.

A cewar wani kakakin Shugaban Somaliyar, za a tura sojoji daga kasashe daban-daban zuwa garin Kismayo, mai muhimmanci ta fuskar tsaro.

Somaliya dai na zargin dakarun Kenya da ke Kismayon da nuna son kai wajen gudanar da aikinsu.

Karin bayani