APGA: Okorocha ya maida martani

Image caption Gwamnan Rochas na jihar Imo

Bangaren gwamnan jihar Imo dake kudu maso gabashin Najeriya, Owelle Rochas Okorocha ya maida martani game da dakatarwar da jam'iyyarsa ta APGA tayi masa.

Ita dai jam'iyyar All Progressive Grand Alliance wato APGA ta ce ta dakatar da gwamnan ne saboda zargin yana mata zagon kasa.

Shi kuwa Gwamna Okorocha cewa yayi ya shiga cikin kawancen jam'iyyun adawar da suka dunkule zuwa jam'iyyar APC ne don amfanin jiharsa.

Har ila yau, bangaren gwamnan na zargin uwar jam'iyyar APGA da kokarin hadewa da jam'iyyar PDP mai mulkin kasar.

Ba wannan bane karon farko da Gwaman a Najeriya zai sauya sheka daga jam'iyyar da aka zabe shi a cikinta zuwa wata jam'iyyar.

Karin bayani