Yarinyar da aka yiwa fyade a India ta rasu

Masu zanga-zanga a India
Image caption Zanga-zanga don neman a hukunta masu aikata fyade a India

A India wata yariya 'yar shekaru goma sha daya ta mutu a asibitin inda take jinyar kunar da aka yi ma ta bayan ta ce, za ta nuna mutumin da ya yi mata fyade.

Yarinyar ta mutu ne da maraicen jiya Lahadi a birnin Calcutta dake arewacin kasar.

Iyayen yarinyar dai sun ce, wanda ya kai ma ta harin ya yayyafa mata kananzir ne domin yana tsoron ta gane shi.

Yarinyar dai sai da ta yi ta fafatawa da mutumin da ya kai mata hari kafin ya ci karfinta.

Koda a watan Satumbar da ya gabata dai an yi zanga-zanga a duka fadin India bayan wata yarinya 'yar shekaru ashirin da uku ta mutu sakamakon fyaden da gungun wasu mazaje suka yi mata.

Karin bayani