Ambaliyar ruwa a Afghanistan da Pakistan

Ambaliyar ruwa a kasar Pakistan
Image caption Ambaliyar ruwa a kasar Pakistan

Ambaliyar ruwa ta mamaye kasashen Afghanistan da pakistan,bayan da aka kwashe kwanaki ana ruwan sama kamar da bakin kwarya.

A gabashin kasashen lamarin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane akalla 80.

Jami'ai sun ce fiye da mutane talatin sun mutu ne a kauyukan da ke gundumar Surobi a gabashin Kabul.

Har yanzu dai ba a gano mutane da dama ba, ya yinda wasu kuma suka bar gidajen su.

A iyakar Pakistan,ruwa ya shafe gidajen al'ummar da ke yankin Khyber Pakhtunkhwa.

Kudancin Karachi na daga cikin wurin da abin ya yi kamari inda mutane goma sha tara suka mutu.