Kotu ta wanke mutane 21 a Turkiya

Image caption Pirayi Ministan Turkey, Recep Erdogan

Wata a Kotu a kasar Turkiya, ta wanke mutane 21 da ake zarginsu da hannu wajen yinkurin kifar da gwamnatin kasar mai kishin Islama.

Har yanzu ana ci gaba da zaman kotun, inda za ta yanke hukunci a kan wasu mutan 254 a cikin shari'ar da aka shafe shekaru biyar ana yi.

Daga cikin wadanda ake zargin hadda shugaban sojin kasar da wasu sojojin, da lauyoyi da malaman jami'a da kuma manema labarai.

Janar Ilker Basbug, wanda ya jagoranci sojin kasar daga shekara ta 2008 zuwa 2010, ya yi watsi da dukan zarge-zargen da ake masa.

Ana zarginsu ne da kokarin kifar da gwamnatin jam'iyyar Justice and Development Party wato AKP.