Amurka za ta ci gaba da rufe ofisoshinta

Daya daga cikin ofisoshin huddar Jakadancin Amurka a rufe
Image caption Ofishin huddar Jakadancin Amurka a Dhaka

Amurka ta ce za ta tsawaita kwanakin rufe kanana da manyan ofisoshin huddar jakadancinta a yankin Gabas ta Tsakiya da gabashin Afirka.

Tace za ta tsawaita rufewar har ya zuwa goma ga watan Ogusta.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta bayyana matakin a matsayin yin kandagarki.

Mahukunta a filin saukar jiragen sama na Heathrow a birnin London, na binciken fasinjoji masu tafiya Amurka, bayan da gwamnatin Amurkar ta bukaci hakan.

Ofisoshin huddar diplomasiayyar Amurkar kimanin 22 ne aka rufe na wucin gadi a cikin kwanaki biyun da suka gabata.

Za dai a sake bude wasu daga cikin ofisoshin huddar jakadancin da suka hada da na biranen kabul da Bagadaza a yau Litinin.