Sojan Amurka ya amsa laifin kisa

Major Hassan Nidal
Image caption Kisan da yayi wa abokan aikin nasa dai shi ne hari mafi muni da aka kaiwa sansanin sojan Amurka ba lokacin ya ki ba.

Wani sojan Amurka wanda ya kashen abokan aikinsa 13 a wani sansanin soji a jahar Texas a shekara ta 2009, ya amsa tuhumar da ake yi masa a kotu.

Major Hassan Nidal wanda likitan kwakwalwa ne na rundunar sojan Amurkar, ya ce shi ne ya harbe mutanen kuma ya roki gafara kan abin da ya kira 'kura-kurai' a daidai lokacinda aka soma yi masa shara'a a wata kotun soji.

Mutumin mai shekaru 42, ya fadawa kotun dake birnin Ford Hood cewar ya aikata hakan ne domin kare Musulmi da kuma kungiyar Taliban a kasar Afghanistan.

Idan aka same shi da laifukan da ake zarginsa, Major Nidal wanda musulmi ne haifaffen Amurka, zai iya fuskantar hukumcin kisa.

Karin bayani