Boko Haram ta aikata laifukan yaki —ICC

Image caption Abubakar Shekau

Mai gabatar da kara ta kotun manya manyan laifuffuka ta kasa da kasa-ICC, ta bayyana cewar, ta yi amannar laiffukan da ake zargin kungiyar Jama'atu Ahlus-Sunna Lid Da'awati Wal Jihad wadda ake kira Boko Haram da aikatawa a Najeriya, sun kai matsayin laifuffukan yaki a kan bil-adama.

Madam Fatou Bensouda ta ce laiffukan sun hada da kashe mutane da cin zarafinsu.

To amma ta ce ba zata kai ga kaddamar da cikkaken bincike ba, sai bayan an kara gudanar da nazari da kuma tantance ko mahukuntan Najeriya su da kansu a shirye suke su gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.

Hakan dai ya fito ne a cikin wani rahoto da ofishin mai gabatar da kara ya fitar, bayan wani bincike da ya gudanar.

Karin bayani