Gobara a filin jirgin saman Nairobi

Jomo Kenyatta International Airport
Image caption Wakilin BBC wanda ke wajen ya ce ya na iya hango hayaki ya turnuke ginin.

Wata gagarumar wuta ta tashi a filin jiragen sama na babban birnin kasar Kenya, Nairobi da sanyin safiyar ranar Laraba.

Sakataren sufari na kasar Michael Kamau yace gobarar ta yi tsanani sosai kuma yayi kira ga jama'a da su yi nesa daga filin jirgin.

Hotunan talabijin sun nuna harsunan wuta suna tasowa daga daya cikin manya gine-ginen da ke filin jirgin.

Wani rahoto yace an kwashe dukkanin mutanen ke ciki. Sai dai babu rahotannin samun rauni ko rasa rai kuma ba a san ko me ya haddasa gobarar ba.

Filin jirgin saman na Jomo Kenyatta dai shi ne babban zango-zangon matafiya ta jirage zuwa yanki gabashin Afrika; inda matafiyan da ke tafiya kasashe masu nisa ke yada zango domin hawan jiragen da zasu kara sa dasu kasashen da za su je.

Karin bayani