An yi zanga-zanga mafi girma a Tunisia

Image caption Kungiyar kwadago ta UGTT ta bukaci 'ya'yanta su dubu dari shida da su shiga zanga-zangar.

Dubun dubatar masu zanga-zanga ne suka kwarara kan tituna a babban birnin kasar Tunisia, wato Tunis, sun neman a rushe gwamnatin kasar.

Ita ce dai zanga-zanga mafi girma da aka yi a birnin na Tunis tun bayan somawar rikicin siyasar kasar na baya-bayanan makonni biyun da suka wuce sa'adda aka hallaka wani fitaccen dan siyasa mai adawa da gwamnati.

Gangamin ya zo ne sa'oi bayan da majalisar dokokin kasar ta jingine zamanta har sai gwamnati da 'yan adawa sun soma tattaunawar sulhu.

Majalisar dai na kan aikin tsara sabon kundin tsarin mulkin kasar ne.

Karin bayani