JTF ta kafa dokar hana fita a Potiskum

Image caption Babban hafsan sojin Najeriya, Janar Ihejirika

Rundunar tabbatar da tsaro-JTF a jihar Yobe ta kafa dokar hana fita ta tsawon sa'o'i ashirin da hudu a karamar hukumar Potiskum na jihar.

A cewar jami'an tsaron dokar za ta fara aiki ne daga ranar Litinin.

Kakakin JTF, Eli Lazarus a sanarwar, ya bukaci al'ummar Potiskum su bada hadin kai ga jami'an tsaro su zauna a gida kada su fito.

Jami'an tsaro sun ce dokar na da manufar tabbatar da tsaro da zaman lafiya, sannan kuma jama'a su ci gaba da baiwa jami'an tsaro bayanan a kan abubuwan da suke da shaku a kai.

Jihar Yobe na daga cikin jihohi uku da Shugaba Goodluck Jonathan ya kakabawa dokar ta baci a watan Mayu.

Karin bayani