China ta ci tarar kamfanoni madara

Image caption Ana cinikin madarar jarirai a China

Gwamnatin China ta ci tarar fiye da dala miliyon dari a kan wasu kamfanonin madarar gari na kasa da kasa guda shidda, wadanda ake zarginsu da magudin tsaida farashi.

Mahukuntan Chinan sun ce, kamfanonin wadanda biyar daga cikinsu na kasashen ketare ne, yayinda gudan kuma na Hong Kong ne, sun yi amfani da wasu hanyoyi na tsaida farashin ba bisa kaida ba.

Kakakin gwamnatin Chinan Xu Kunlin, ya ce "bayan kammala bincike, mun samu tabbacin cewa wadannan kamfanonin sun keta dokar kasar China wadda ta haramta yin babakere a harkokin kasuwanci".

'Yan China na matukar bukatar madarar gari ta yara wadanda aka yi a kasashen wajen tun a shekara ta 2008, da wasu yara shida suka mutu bayan sun sha madarar da aka yi a cikin gida.

Karin bayani