Ana shakku kan sasanta rikicin Masar

Sanatocin Amurka a Masar
Image caption Sanatocin Amurka a Masar

Masu shiga tsakani na kasashen waje sun bayyana fargabar cewa, yunkurin sasanta rikicin Masar ba zai yi nasara ba.

Wani dan majalisar Amurka ya yi gargadin cewa 'yan kwanaki ya rage kafin a kai ga zubar da jini.

John McCain da sanata Lindsey Graham sun bukaci gwamnatin Masar da ta saki fursunonin siyasa, tare da tattauna wa da kungiyar 'yan uwa musulmi.

Sai dai shugaban rikon kwarya Adly Mansour, ya yi gargadin cewa ba za su lamunci shisshigi a harkokin cikin gidansu ba.