Yunkurin sasantawa ya ci tura a Masar

Masu zanga zanga a masar

Gwamnatin wucin gadin kasar Masar ta ce yunkurin kasashen waje na sasanta takaddamar siyasar kasar ya ci tura.

Ta dora alhakin gazawar yunkurin, kacokan kan kungiyar yan uwa musulmi.

Hukumomin sun kuma kara yin gargadin cewa za su tarwatsa dukkanin dandali guda biyo a birnin Alqahira da magoya bayan hambararren shugaban kasar Muhammad Morsi ke zarga zangar zaman dirshen a cikinsu.

Karin bayani