Safarar hauren giwa zuwa China

Hauren da aka kama a Hong Kong
Image caption Hauren da aka kama a Hong Kong

Jami'an kwastum a birnin Hong Kong a China, sun cafke wani jirgin ruwa mai dauke da haramtattun hauren giwa daga Najeriya.

Haramtattun kayayyakin da aka boye a jirgin ruwan da ya taso daga Najeriya, sun hada da hauren giwa da dorinar ruwa da karkanda da kuma fatun damusa.

Kuma jami'ai a Hong Kong sun gano su ne boye a cikin wasu akwatuna 21, a kwantenar dake cike da katakai.

Darajar hauren da fatun da aka samu sun kai dalar Amurka sama da miliyan biyar.

Hukunci

Sai dai jami'an Hong Kong ba su kama kowa ba a game da safarar haramtattun kayayyakin.

Amma a karkashin dokar birnin duk wanda aka samu da laifi, za a daure shi na tsawon shekaru biyu ko a ci tararsa dalar Hong Kong miliyan biyar.

A watan da ya gabata dai hukumomin birnin sun kama hauren giwa 1,000.

Masu fafutukar hana fasa-kwaurin dabbobin da aka hana safararsu sun ce, tasirin China a nahiyar Afrika ne ya janyo karuwar fasa-kwaurin kayayyakin.

A mafi yawancin lokuta a kan kai su China ko kasar Thailand, domin yin kayan ado na hauren giwa da makamantansu.