Areva ya koma hako Uranium a Arlit

Image caption Kamfanin Areva

Kamfanin ma'adinai na Faransa-Areva ya koma ayyukansa na uranium a Somair dake arewacin Nijer, bayan an samu cikas sakamakon harin dan kunar bakin wake a watan Mayu.

Hukumomi a Nijer sun ce an dakatar da ayyuka na makwanni shida, a Somair daya samarda tan dubu uku na Uranium a shekara ta 2012.

Rufe kamfanin Areva dake Arlit ya janyowa kamfanin hasarar fiye da dala miliyon 36.

Kamfanin Areva ya dakatar da ayyukansa ne a ranar 23 ga watan Mayu bayan dan kunar bakin wake ya kashe mutum daya tare da raunata wasu goma sha hudu.

Kamfanin Areva shine ya mallaki kashi 64 cikin 100 na Somair a yayinda gwamnatin Nijer keda kashi 36 cikin 100.

Karin bayani