Agogo komai da ruwanka na Samsung

Zanen agogo komai da ruwanka na Samsung
Image caption Zanen agogo komai da ruwanka na Samsung

An samu bayanai game da agogo komai da ruwanka da kamfanin lataroni na Samsung ke son kerawa.

Zane-zanen da aka samu na nuna agogon hannu dake da fuska mai laushi, da za a iya lankwasa wa, kuma igiyar agogon na karfe ne.

Za ka iya ganin wanda ke kiran wayar salularka ta manhajan agogon.

Sannan za ka iya karanta sakonnin shafukan Twitter da facebook ta agogon hannun.

Haka kuma za a iya kiran waya ko amsa waya ta agogon da za a hada da hanyar sadarwa ta intanet.

Sharhi

Masu sharhi na ganin za a samu bunkasar kasuwar agogo komai da ruwanka, daga dubu 330 da aka fitar zuwa kasashen waje a bara zuwa miliyan biyar a shekarar 2014.

Sai dai wani masani a harkar wayoyin tafi da gidanka, Francisco Jeronimo da ganin karamar fuskar da agogon ke da ita zata sanya ba lallai ba ne manhajoji su yi tasiri.

Samsung zai yi gasa da wasu kamfanonin lataroni da suma tuni suka bayyana aniyar kera agogo komai da ruwanka a farkon shekarar nan.