Eid: An kashe mutane 14 a Afghanistan

Image caption Mutum yana goge jini

Mata da kananan yara da dama sun mutu bayan da bam ya tashi a wata makabarta dake gabashin Afghanistan.

Kakakin gwamnan lardin Nangarhar, ya shaidawa BBC cewar akalla mutane goma sha hudu sun gamu da ajalinsu sakamakon harin.

Mamatan sun taru ne a makabarta don jana'izar matar wani shugaban kabila, a cikin bukukuwar Eid al-Fitr bayan kamalla azumin watan Ramadana, sai aka taba bam a wurin.

A jawabinsa bayan idar da Sallah a Kabul, Shugaban Afghanistan, Hamid Karzai ya bukaci 'yan Taliban su daina kashe mutanen da basu ji basu gani ba.

Sannan ya bukacesu su shiga adama dasu a cikin siyasar kasar.

Karin bayani