An gano rigakafin cutar maleriya

Image caption An wallafa sakamako binciken ne a mujallar kimiyya ta ''Science''.

Wasu masu bincike da ke kokarin samar da allurar riga-kafin zazzabin cizon sauro sun wallafa sakamakon gwajin da suka yi wanda ya nuna cewa akwai alamun allurar za ta yi tasiri.

Masana kimiyyar dake a Amurka sun gano cewa dan adam na samun karin garkuwan-jiki idan aka yi masa allurar kwayar cutar maleriya wadda aka raunana.

Suka ce jikunkunan wasu mutane shida da suka amince aka saka musu kwayar cutar da aka sarrafa, sun samu garkuwa daga cutar ta Maleriya.

Sai dai jagoran masu binciken ya ce wannan gwajin yayi kadan kwarai kuma akwai bukatar a kara yin aiki a kai.

Karin bayani