Mummunan Fari a Namibia

Image caption Sai dai a yanzu gwamnatin ta soma rarraba abinci ga yankunan karkara.

Kasar Namibia wadda ta fi kowace kasa a kudancin Afrika fuskantar hamada tana fama da farinda aka ce shi ne mafi muni a cikin shekaru talatin.

Wurin da lamarin yafi kamari dai shi ne yankin Kunene da ke shiyar arewa maso yammacin kasar, inda al'ummar makiyaya ta Himba ke cikin shekara ta biyu ba tare da ganin ruwan sama ba; abin da ya haddasa matukar karancin ciyawa da ruwan kiwon shanun da suka dogara a kai.

Ruwan da ke cikin manyan madatsun ruwan da ke baiwa kasar ruwa dai za iya karewa idan ba a samu saukar damina cikin lokaci ba; kuma riyoji da rafukan da ke karkara sun riga sun kafe.

Wani waikilin BBC a can yace ''Yara sun fara daina zuwa makaranta saboda sun galabaita kuma ba su da abin da za su ci mai sa kuzari''.

Neman agajin kasa-da-kasa

Yanzu haka dai gwamnatin kasar ta mika kokon baranta ga kasashen duniya domin neman abin da za ta tallafawa wadanda ke cikin tsananin bukata kafin a sami ruwan sama.

Watanni biyu da suka wuce, shugaban kasar Hifikepunye Pohamba ya yi shelar kafa dokar-ta-baci kuma duk da raba abinci da akayi ta hannun kwamitin kula da masu bukatar gaggawa ta kasar, kusan mutane dubu 400, daga cikin al'ummmar kasar su miliyan 2 da dubu 300 za su iya fuskantar yaunwa.

An dai soki gwamnatin kasar da bayarda tallafin da baya isa matuka kuma a makare. Kuma ana jin koke-koken cewar tallafin baya isa ga wadanda suka fi bukatar sa.

Sai dai a yanzu gwamnatin ta soma rarraba abinci ga yankunan karkara kuma kasashen kamar su Rasha da China sun soma amsa kiran da kasar tayi ga kasashen duniya na su bata tallafi.

Karin bayani