Dan sanda ya rasa aikinsa saboda rashawa

Image caption Dan sandan Najeriya wanda aka kora

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kori wani dan sanda wanda aka dauki hoton bidiyonsa yana kokarin karbar cin hanci daga wajen wani mai mota.

Dan sandan na kokarin karbar dala dari da sittin ko kuma naira dubu ashirin da biyar daga wajen wani mai mota, daya saba ka'idar tuki a kusada filin saukar jiragen sama a Legas.

Dan sandan bai san cewar ana daukar hoton bidiyonsa ba, ya shiga cikin motar mutumin suna cinikin nawa za a bashi a matsayin na 'goro'.

Dubban mutane ne suka kalli hoton bidiyon a intanet ta hanyar YouTube, kuma gidajen talabijin da dama sun dauki hoton bidiyon.

Kungiyar sa'ido ta kasa da kasa wato Transparency International ta bayyana Najeriya a matsayin kasar dake gaba-gaba wajen cin hanci da karbar rashawa.

Karin bayani