Amurka ta kai hari a Yemen

Image caption An kai hare-hare irin wadannan har sau bakwai a Yemen daga watan Yuli zuwa yau.

Jami'an sojin Yemen sun ce wasu hare-hare da wani jirgi maras matuki na Amurka ya kai a cikin kasar ya hallaka wasu da ake jin mayakan sakai ne akalla 14 ranar Alhamis.

Jami'an suka ce jirgin ya kai hari har sau uku ne kan wasu cibiyoyin mayakan da ke kudancin kasar.

A cikin watanin nan dai Amurka ta kara kaimi wajen kai hare-hare da jirage marasa matuki kan wadanda ake tuhumar 'yan kungiyar Al_qaeda ne a kasar.

A farkon wannan makon an rufe ofisoshin jakadancin Amurka da wasu kasashen yamma da ke Yemen din saboda fargabar kai musu hare-hare, kuma a ranar Laraba hukumomin Yemen din suka ce sun wargaza wani shirin kai hari kan matatun mai da tashoshin jiragen ruwa da kungiyar ta tsara.

Karin bayani