Zargin fasakaurin jarirai a China

China
Image caption Ana zargin likitoci da sata da kuma sayar da jarirai a China

'Yan sanda a China sun bada rahotan cewa sun tsare wasu mutane tara da ake zargi da yin fasakaurin jarirai a wani asbiti dake lardin Shaanxi.

An ruwaito cewa an kori wasu jami'an gwamnatin yankin su uku da kuma jami'an asibitin su uku.

Matakin ya biyo bayan kokarin da 'yan sanda suka yi na ceto wasu tagwayen jarirai mata da kuma wani jariri guda , wadanda akai zargin cewa wani likita ne ya sace su, ya kuma sayar dasu, bayan da ya yiwa iyayen jariran karyar cewa suna fama da wata matsananciyar rashin lafiya.

'Yan sanda sunce sun sami rahotanni hamsin game da irin wannan lamari na fasakaurin kananan yara.

Karin bayani