Obama ya yi bayani game da tattara bayanan sirri

Shugaba Obama na Amurka
Image caption Ana son Amurkawa su fahimci aikin tattara bayanai

Shugaba Obama na Amurka ya bayyana shirye shiryen da zasu fito fili su bayyana shirin aikin leken asirin Amurka ba tare da wani boye boye ba.

Yayinda yake jawabi a wani taron manema labarai, Mr. Obama yace ba shi kadai bane ya kamata ace yana da kwarin gwiwa game da shirye shiryen, haka suma Amurkawa ya ce na bukatar wannan kwarin gwiwar.

Tun lokacin da tsohon jami'in leken asirin Amurka Edward Snowden ya tona asirin shirye shiryen da Amurka ke yi na sauraron wayoyin jama'a ne gwamnatin Obaman ke ta kokarin ganin ta nunawa jama'a hujjar ta na yin hakan.

Mr. Obama ya ce yana son ya gamsar da wadanda ke ganin rashin alherin shirin.

Karin bayani